Babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin hulda da manema labarai, Mista Femi Adesina ya bayyana cewa, ma su sababba rikici, tayar da tarzoma gami da kawo zagon kasa ga zaman lafiya sai sun kunyata a kasar nan.
A ranar Talatar da ta gabata ne Mista Adesina ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin mambobin gidauniyar Orji Kalu da kuma kungiyar JCI (Junior Chamber International) a fadar shugaban dake babban birnin tarayya na Abuja.
Femi Adesina, Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da kuma Shugaba Buhari
Femi Adesina, Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da kuma Shugaba Buhari
Hadimin na shugaban kasa yake cewa, "ga masu yiwa zaman lafiyar kasar nan zagon kasa, su sani cewa ba za su taba cimma nasara ba."
"Za a samu zaman lafiya a Najeriya, kuma idan ma su aikata mugun nufi ba su amince da tabbatuwar hakan ba, to kuwa za a zauna lafiya ba tare da su ba."
A cewar sa, ya kamata bambance-bambance addinai, kabilanci, al'adu, yaruka da kuma siyasa su kara dankon zumantar mu a madadin rabuwar kawanunan mu wajen zubar da jinin juna.
A yayin wannan taro, Honarabul Damian Igbokwe ya yi jawabai a madadin tsohon gwamnan jihar Abia kuma babban jigo na jam'iyyar APC, Cif Orji Kalu, wanda ya kasance jagora cikin wannan tafiya ta wanzar da zaman lafiya a kasar nan.
Mista Kalu ya bayyana takaicin sa dangane da yadda tashin-tashina ke ci gaba da kunno kai a kasar nan cikin shekarun da suka shude ta sababin kiyayya ta addinai, kabilanci, rashin hadin kai, rashin tsaro, wahalar rayuwa da makamantan su.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa, harkar tsaro ta shafi kowa da ya kamata a hada kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.