'LABARAI DAGA 24BLOH
Salihu Takai zai yi takara duk da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya tsaida mutanen sa da za su nemi kujerar Gwamnan a PDP. Kwankwaso dai ya zabi 'Yan Kwankwasiyya ne su kara da Gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje a zaben 2019.
Kwankwaso ya dauko tsofaffin kwamishinonin sa Abba Kabir Yusuf da Ahmad Abdulsalam su fito takarar Gwamna da Mataimakin sa ne a Kano. Duk da haka Malam Salihu Takai ya nuna cewa ba zai fasa shiga zaben fitar da gwani da. 
Kwamitin yakin neman zaben Takai ta tabbatar da cewa a shirye 'Dan takarar yake da ya goga da wanda Kwankwaso ya tsaida wajen neman tikitin Jam'iyyar PDP. A karshen makon nan ne aka tantance Takai a matsayin 'Dan takarar Gwamna a Kaduna.
Kwanaki ne dai Uwar Jam'iyya ta rushe Shugabancin PDP a Kano aka nada wani 'Dan Kwankwasiyya a matsayin Shugaban rikon kwarya. Wannan ya sa Shekarau ya koma APC amma irin su Takai su ka bi Kwankwaso su na sa ran samun tikiti.
Salihu Takai tsohon Kwamishi na a Gwamnatin Shekarau wanda ya dade yana neman Gwamna. Takai ya dade a PDP kafin Kwankwaso da jama’ar sa su bar Jam’iyyar APC kwanaki.