Full width home advertisement

Travel the world

Climb the mountains

Post Page Advertisement [Top]

Abubuwan hadawa
  • Falawa kopi 3 
  • Bota 1
  • Kwai 3
  • Mangyada
  • Suga rabin kofi
  • Gishiri rabin cokali
  • Yeast cokali daya
  • Baking hoda cokali 1
Yanda ake hadawa
  1. Da farko zaki tankade fulawarki a kwano mai fadi.
  2. Sai ki sa yeast da baking hoda ki juya, sai ki sa bota ki yi ta juyawa ya hadu da fulawan sosai.
  3. Sai ki fasa kwanki ki zuba ki juya ya hadu da fulawan.
  4. Sannan sai ki zuba suganki a ruwan dumi ki juya sai ki zuba a fulawar ki kwaba da dan gishiri.
  5. Idan yayi sai ki rufe ki sa a rana yayi kamar minti arba'in.
  6. Sai ki duba idan ya tashi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada.
  7. Sai kuma ki kawo gwangwanin madara na ruwa don ki samu yayi rawun sai ki sa a paranti ki dinga murzawa kina sa wannan gwangwanin kina fitar da rawun din donut dinki, kuma ki na sawa a mai kina soyawa, hakan zaki yi tayi harki gama.

No comments:

Post a Comment

Bottom Ad [Post Page]

| Designed by 24blog Inc | Distributed By 24blog